
Hadarin mota ya halaka mutane sama da 20 a cote d'ivore
Play all audios:

Hukomomin kasar Cote d'Ivore sun tabbatar da mutuwar mutane 21 tare da jikkatar wasu 10, sanadiyyar hadarin mota da ya ritsa da su cikin daren Lahadi. Sanarwar da ma'aikatar
sufurin kasar ta fitar a Litinin din nan ta ce tuni ta kaddamar da binciken musabbabin faruwar hadarin, sannan ta gargadi masu ababen hawa da sun rinka kiyaye dokoki da ka'idojin kan
hanya, don kare rayuka da dukiyoyin al'umma. Karin bayani:Shugaba Ouattrara ya tsige firaministansa Ko a farkon shekarar nan wata tankar dakon mai ta banke motar bas mai dauke da
fasinjojin a arewacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13, wasu 44 kuma suka samu raunuka.